Ana zargin matashin mai shekaru 27 mai suna Kabiru Nuhu ya zubawa mahaifinsa nasa fetur daga bisani kuma ya kunna masa wuta.
Zuwa yanzu ba a san dalilinsa na aikata hakan ba, amma dai rundunar yansandan jihar Jigawa ta ce tana ci-gaba da bincike.
A wani bayani da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Shiisu Lawan Adam ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 1 ga watan Aprilu da muke ciki a yankin Lokon Malami dake garin Kazaure.
Adam ya ce yansanda sun samu kiran gaggawa da misalin karfe 6 na safe, tare da sanar da su cewa wani ya cinnawa dattijon wuta.
Nan take aka tura jami’ai zuwa yankin, inda aka garzaya da dattijon zuwa asibiti.
Binciken yansanda ya kai ga kama wanda ake zargin bayan an ganshi da kunar wuta a goshi da hannu da kuma kafa, lamarin da ya sa ake zargin akwai hannunsa a wannan aika-aikar.