NE

News Elementor

Zazzaɓin Lassa Ya Kashe Mutum 146 A Najeriya

Barkewar zazzabin Lassa da ake samu a Najeriya na nuna karuwar mace-mace mai tayar da hankali, inda sabbin alkaluma daga cibiyoyin jinya da sa ido na kasa ke nuna cewa ba yaduwa kadai ake samu ba har ma da karin mace-mace a jihohi da dama.

Sabbin alkaluma daga hukumar dakile cutuka masu yaduwa da ta kasa (NCDC) sun nuna cewa an samu sama da mutum 500 da aka tabbatar sun kamu da cutar da kuma wadanda suka mutu 146 tsakanin watan Janairu zuwa tsakiyar Maris din nan.

Haka kuma NCDC ta ce akalla ma’aikatan lafiya 38 sun kamu a wannan barkewar, inda akalla uku suka mutu — abin da masana ke cewa yana nuna hadarin aikin su da kuma gazawar tsarin kariya daga kamuwa da cutar.

Rahoton ya nuna cewa yawan mace-mace ya kai kashi 25.1, wanda ya fi kashi 18.7 da aka samu a irin wannan lokaci a shekarar 2025, lamarin da kekara nuna cewa ana samun karin masu kamuwa na mutuwa duk da kokarin da ake yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM