Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ba da umarnin rusa wata haramtacciyar unguwa da ke kusa da Karmajiji a yankin Kukwaba na Abuja, bayan rahotannin sirri sun danganta wurin da maboyar masu aikata laifuka.
Wike ya bayar da umarnin ne bayan taron kwamitin tsaro na Abuja, inda ya jagoranci jami’an tsaro zuwa duba yankin.
Ya ce ana zargin masu laifi na komawa wurin bayan sun aikata hare-hare a sassan Abuja.
Ministan ya bayyana cewa rashin tsari a unguwar na hana jami’an tsaro gano ko bibiyar mazauna yankin, yana mai cewa hakan babbar barazana ce ga tsaro.
Ya umarci sashen kula da tsare-tsaren gine-gine na FCT tare da hadin gwiwar Kwamishinan ‘yansndan Abuja, Ahmed Sanusi, su gaggauta rusa unguwar.
Wike ya ce matakin wani bangare ne na kokarin gwamnatin FCT na kawar da maboyar masu laifi, inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar babban birnin tarayya.