NE

News Elementor

Tawagar Kano ta gana da sakataren gwamnatin tarayya don neman a saki kuɗin tallafi ga ƴan kasuwar Singer da gobara ta shafa

Wata babbar tawaga ta ‘yan kasuwa da manyan jami’an gwamnatin Jihar Kano ta gana da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, domin neman a gaggauta sakin tallafin Naira biliyan 5 da Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin bai wa waɗanda gobarar Kasuwar Singer ta shafa.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce tawagar ta kai ziyarar ne domin tunatar da Gwamnatin Tarayya alkawarinta na tallafa wa dubban ‘yan kasuwar da gobarar ta lalata musu shaguna da hanyoyin samun abinci.

Tawagar ta bayyana cewa sakin tallafin cikin gaggawa zai taimaka wajen farfaɗo da kasuwancin waɗanda abin ya shafa tare da dawo da harkokin kasuwanci a kasuwar.

Mambobin tawagar sun gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da tallafin, tare da roƙon a kammala dukkan matakan fitar da kuɗin domin waɗanda abin ya shafa su amfana ba tare da ƙarin jinkiri ba.

Tawagar ta haɗa da Shugaban Ƙungiyar Ƴan Kasuwar Kano, Alhaji Sabiu Bako; Kwamishinan Kuɗi na Jihar Kano, Dakta Isma’il Aliyu Danmaraya; APC National Ex-Officio, Muhammad Jamu Yusuf; Shugaban Kasuwar Singer, Barrista Junaidu Muhammad Zakari; da ɗan kasuwa Alhaji Kabiru Adamu Gano.

A nasa jawabin, Sanata George Akume ya tabbatar wa tawagar cewa Gwamnatin Tarayya na ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa waɗanda gobarar Kasuwar Singer ta shafa.

A baya dai Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya sanar da amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bayar da tallafin Naira biliyan 5 ga gwamnatin Kano domin tallafa wa waɗanda gobarar Kasuwar Singer ta shafa. Haka kuma ya ce Ƙungiyar Gwamnonin APC ta yi alƙawarin ƙarin Naira biliyan 3 domin tallafa wa waɗannan ‘yan kasuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM