
Yan bindiga sun tayar da kauyuka akalla 30 a gundumar danchadi dake karamar hukumar Bodinga ta jihar Sokoto.
Hare-haren da aka kaddamar a tsakanin Laraba da Alhamis, sun haddasa kisan mutum 6, da raba daruruwan jama’a da muhallansu, da kuma sace dabbobi fiye da 1000.
Hakan dai na kunshe ne a wani rahoto da Uban kasar Danchadi, Alhaji Lirwani Mafaran Kuwarun Sarkin Musulmi, ya aikewa shugaban karamar hukumar Bodinga.
An kuma aike da kwafin wannan rahoton zuwa ga baturen yansanda na yankin, da hukumar Civil Defense, da kuma hukumar DSS.Rahoton ya ce yan bindiga sun kashe mutum 6 a kauyukan Kyaluje da Dibarke, tare da sace dabbobi 1000, ciki har da shanu da rakuma.
Kauyukan da yan bindigar suka tayar sun hada da Gidan Gadanga, Gidan Dan Bube, Dutsin Mai Gunya, Batsauje, Sire Modi, Gwantsi, Kore Maiganga, Bangi Rafi, Bangi Dutsin, Yabawa, Lageji, Bille, Gonin Gari, Wumumu, Chohi, Saran Malan, Wure Yal’dde, Gidan Hodi, Dabugi, Rukusawa, Tunga, Lakes, Maikataru, Dutsin Toka, Karaje, Kwantsi Buga, Yan Gidaje, Runbuki, Kwantsi Tunga da kuma Lau Gari.