Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta gayyaci wani ɗan siyasa, Hon. Aminu Abdullahi Warkal, domin yi masa tambayoyi kan zargin nuna bindiga ba bisa ƙa’ida ba a lokacin wani taro da ake zaton na siyasa ne.
Rundunar ta ce ta ci karo da wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta yayin da take gudanar da sintirin yanar gizo na yau da kullum, inda ake zargin an ga Warkal yana nuna bindiga a fili, wadda ake kyautata zaton bindiga ce mai ɗaukar harsasai da yawa.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar Litinin, ‘yan sandan sun ce idan aka tabbatar da zargin nuna bindigar, hakan na iya zama saɓa wa tanade-tanaden dokar mallakar makamai da bindigogi.
Rundunar ta ce irin wannan ɗabi’a na iya kuma “janyo tsoro, tsoratar da jama’a da kuma kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron al’umma.”
A cewar sanarwar, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin a gayyaci Warkal zuwa hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano, domin yi masa tambayoyi.
Ta ƙara da cewa a halin yanzu Warkal yana sashen tattara bayanan sirri na rundunar, inda ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
‘Yan sandan ba su bayyana ko an kwato bindigar da ake zargin an nuna a cikin bidiyon ba, ko kuma ko Warkal ya bayar da bayani kan dalilin da ya sa yake da bindigar ko kuma ya nuna ta.
Rundunar ta yi gargaɗin cewa ba za ta amince da ayyukan rashin bin doka, daba ko kuma nuna makaman da ka iya yin barazana ga zaman lafiyar jama’a ba, ba tare da la’akari da matsayin mutanen da abin ya shafa ba.