NE

News Elementor

‘Yan sanda sun kama daya daga cikin manyan barayin daji a jihar Kano

Rundunar ’yan sandan Kano ta kama wani mutum da ake zargi daya ne daga cikin ɓarayin daji a karamar hukumar Bichi, inda ta kwato harsasai 109 da kuma wasu kayayyakin da ake zargin za a kai wa ’yan bindiga.

Mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

A cewar sanarwar, jami’an ’yan sanda na sashen Bichi sun samu sahihan bayanai a ranar Asabar cewa wani mutum sanye da kayan sojoji da ake zargi da na bogi ya an ganshi a ƙauyen Rimaye da ke karamar hukumar Bichi.

Jami’an, tare da haɗin gwiwar wasu mazauna yankin Rimawa, sun yi nasarar cafke wanda ake zargin mai suna Mohammed Isah Haruna, mai shekara 28, mazaunin Dan Dinshe Yamma Quarters a karamar hukumar Dala ta jihar Kano.

Binciken jakarsa anga bindiga AK-47 guda ɗaya mai ɗauke da harsasai 30, da kuma wasu harsasai 79 na AK-47.

Haka kuma, ’yan sandan sun kwato kayan sojoji guda biyu, hulunan sojoji guda uku, katin shaidar soja na bogi da ake zargi, katin shaida na ƙasa, takardar NIN, katin zaɓe, katunan ATM guda huɗu da takalman sojoji.

Rundunar ta ce wanda ake zargin ya amsa yayin bincike cewa ya je yankin ne domin kai kayayyakin da aka kwato ga ’yan bindigar da ke aiki a cikin daji.

Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar Rimawa bisa samar da bayanan sirri da suka taimaka wajen cafke wanda ake zargin.

Ya ce haɗin gwiwar al’umma da jami’an tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da miyagun laifuka, yana mai jaddada cewa tsaro nauyi ne da ya rataya a kan kowa.

Rundunar ta ce wanda ake zargin yana hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano tare da cafke sauran mambobin ƙungiyar masu aikata laifukan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM