NE

News Elementor

‘Yan bindiga sun sace daliban da ke rubuta NECO a jihar Kogi

Rundunar ƴansandan jihar Kogi ta tabbatar da yin garkuwa da ɗalibai huɗu da ke rubuta jarrabawar NECO da wasu malamai biyu cikin har da shugaban makarantar.

Cikin wata sanarwar kakakin rundunar ƴansandan jihar ASP Salisu Oyiza ta fitar ta ce lamarin ya faru ne ranar Talata da yamma lokacin da ɗaliban ke tsaka da rubuta jarrabawar NECO a makarantar Sakandiren Edo-Ekina da ke yankin ƙaramar hukumar Dekina.

Ƴansan sun kuma ce sun kai ɗaukin gaggawa tare da ƙaddamar da bincike kan lamarin.

Tawagar hadin giwar jami’an tsaro sun gaggauta ƙaddamar da neman ɗaliban, waɗanda har yanzu kuma suna neman jami’an, in ji sanarwar.

ASP Oyiza ta ce zuwa yanzu jami’an tsaro sun kuɓutar da ɗalibi ɗaya, yayin da suke ci gaba da neman sauran tare da farautar maharan.

Lamarin na zuwa kwanaki bayan kuɓutar da ɗaliban makarantar jihar Oyo da suka kwashe makonni a hannun ƴanbindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM