NE

News Elementor

’Yan Sanda Sun Kama Wata Mota Cike Da Kakin soja Da Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Legas

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kama buhuna 47 na kayan sojoji da kuma kwalaye 80 na miyagun ƙwayoyi da ake zargi a wani samame da ta gudanar a yankin Surulere.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Fatai Tijani, ya bayyana cewa jami’an rundunar sun kuma kama wasu mutum uku da ake zargi da hannu a lamarin yayin aikin da suka yi bisa bayanan sirri.

Wadanda aka kama sun hada da Chinedu David mai shekara 29 da haihuwa, Ezeagwu Chukwuma mai shekara 38 da Ifeanyi Ogbeanyi mai shekara 45. An kama su ne tare da wata babbar motar dakon kaya da ba ta da rajista wadda ke ɗauke da kayan.

Binciken farko ya nuna cewa ana zargin motar na jigilar kayan sojojin ne zuwa yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, yayin da kwalayen da aka samu a cikinta ake zargin suna ɗauke da miyagun ƙwayoyi.

Kwamishinan ya ce bincike na ci gaba domin gano inda kayan suka fito, masu su da kuma mutanen da ake son kai wa, tare da gano sauran waɗanda ke da hannu a lamarin.

Ya kuma tabbatar wa mazauna Legas cewa lamarin ba ya barazana kai tsaye ga tsaron jihar, domin ana zargin kayayyakin na kan hanyar fita ne daga Legas zuwa wani yanki na ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM