Wata ‘yar Najeriya da ke zaune a ƙasar Canada, Ezinne Nwanorue, ta zargi mijinta, Franklin Nwanorue, da ci gaba da yin lalata da wata mata duk da rantsuwar da ya yi a bainar jama’a cewa ba zai taɓa cin amanarta ba.
Ezinne ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Alhamis, inda ta ce ta sha wahala a hannun mijinta duk da cewa shi ne ya ɗauki nauyin tafiyarta zuwa Canada.
Ma’auratan sun jawo hankalin mutane a kafafen sada zumunta a farkon makon nan bayan sun wallafa bidiyon da suke rantsuwa cewa ba za su yi zina ba, tare da roƙon Allah ya ɗauki ran duk wanda ya karya alkawarin.
A cikin bidiyon, Franklin ya ce idan ya isa Canada ya ci amanar matarsa, Allah Ya ɗauki ransa, yana mai cewa matarsa ce ta nemi yin wannan rantsuwa bisa umarnin Allah domin kare aurensu.
Ita ma Ezinne ta wallafa nata bidiyon inda ta yi irin wannan rantsuwa, tana alƙawarin kasancewa mai aminci ga mijinta.
Sai dai daga baya, Ezinne ta wallafa wani saƙo da ta ce ya fito daga wata mata da take zargin ƙawar mijinta ce, wadda ta yi ikirarin cewa Franklin ya ci gaba da hulɗa da ita ko da bayan rantsuwar da ya yi.
Ezinne ta ce abin da kawai take bin mijinta shi ne ya kammala mata takardun biza, tana mai ƙara da cewa ta yi imanin Allah zai yi hukunci idan mijinta ya karya rantsuwar da ya yi na kasancewa mai aminci a aurensu.