Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta amince wa Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta rusa wani ɓoyayyen masana’antar ƙera ƙwayar sinadarin methamphetamine, wani nau’in miyagun ƙwayoyi.
Wurin da ake zargin ana sarrafa ƙwayoyin yana cikin ƙauyen Iloti da ke dajin Abidagba a ƙaramar hukumar Ijebu East ta Jihar Ogun.
Mai shari’a Musa Kakaki ya ba da umarnin rushe wurin tare da lalata wasu sinadarai da aka ƙwato daga hannun wasu ‘yan ƙasar Mexico uku da kuma ‘yan Najeriya bakwai da ake tuhuma da gudanar da haramtacciyar masana’antar.
Sai dai kotun ta hana lalata wasu sinadarai da ake taƙaddama a kansu bayan lauyoyin waɗanda ake zargin sun nuna adawa, suna mai cewa sinadaran na iya zama muhimman hujjoji a shari’ar.
NDLEA ta bayyana cewa sinadaran da aka gano suna da haɗari ga lafiyar jama’a kuma darajarsu ta kai kusan naira biliyan 480.
Bayan sauraron hujjojin ɓangarorin biyu, kotun ta amince da buƙatar rushe wurin amma ta ɗage shari’ar zuwa ranakun 26, 27 da 28 ga watan Oktoba domin ci gaba da sauraron shari’ar da kuma yanke hukunci kan wasu sinadaran da ake gardama a kansu.