Darektan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce shugaba Bola Tinubu na da ƙarfin siyasar da zai ba shi damar lashe jihohi sama da 20 a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Yari ya bayyana cewa za a ƙaddamar da ƙungiyar yaƙin neman zaɓen APC a ranar 14 ga Oktoba, yayin da za a fara gangamin zaɓen a hukumance a Kaduna a ranar 24 ga Oktoba, kafin a kai ziyara sauran jihohin ƙasar.
Ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda ya ce shugaban ƙasar ya amince da jadawalin rangadin jihohin da za a gudanar domin neman goyon bayan sake zaɓensa.
Yari ya kuma yi watsi da yiwuwar ‘yan takarar adawa, Peter Obi na jam’iyyar NDC da Atiku Abubakar na ADC, su kayar da Tinubu, yana mai cewa babu ɗayansu da ke da cikakken iko a jihohin da ke wajen yankunansu.
A cewarsa, babu ɗan takarar da zai iya lashe zaɓen shugaban ƙasa ta hanyar dogaro da goyon bayan yanki guda kawai, domin samun nasara na buƙatar goyon baya daga Arewa da Kudu.
Ya yi misali da zaɓen shugaban ƙasa na 2011, inda marigayi Muhammadu Buhari ya samu gagarumin goyon baya a Arewa amma bai yi nasara a matakin ƙasa baki ɗaya ba.
Yari ya ƙara da cewa Tinubu ya samu nasarorin da APC za ta yi amfani da su wajen yaƙin neman zaɓen 2027, yana mai cewa jam’iyyar za ta fi mayar da hankali kan ayyukan da ta gudanar maimakon yin sabbin alkawura.
“Ba alkawura muke yi ba. Muna aiwatar da ayyuka, kuma za mu ci gaba da hakan,” in ji Yari.