NE

News Elementor

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Sowore, ya buƙaci a halasta noman wiwi a Najeriya

Ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin bil’adama kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya soki Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, kan lalata gonakin tabar wiwi a Jihar Edo, yana mai kira da a halasta tare da tsara yadda ake noman tabar wiwi a Najeriya.

Sowore, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, ya soki hukumar kan lalata abin da ya bayyana a matsayin amfanin gona mai matuƙar amfani ga tattalin arziki, a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsanancin talauci.

Ya ce ya kamata gwamnati ta daina lalata gonakin tabar wiwi, maimakon haka ta halasta noman ta tare da tsara shi domin amfani da damar da take da ita a fannonin magunguna da masana’antu.

Sowore ya ce Najeriya za ta iya samun moriyar tattalin arziki daga masana’antar tabar wiwi da aka tsara yadda ya kamata, ta hanyar gudanar da bincike, samar da ayyukan yi da kuma ƙara samun kuɗaɗen shiga ga gwamnati.

Ya ce, “Ku halasta kuma ku tsara yadda ake noman tabar wiwi yadda ya kamata. Ku saka ido a bincike, ku yi amfani da damarmakin da take da su wajen samar da magunguna da kayayyakin masana’antu, ku samar da ayyukan yi, ku samar da kuɗaɗen shiga, sannan ku gina masana’antar da ’yan Najeriya za su amfana da ita.”
Sowore ya kuma ce bai kamata a yi amfani da lalata gonakin tabar wiwi a matsayin hanyar yaƙi da talauci ba, yana mai sukar manufar da NDLEA ke bi a halin yanzu.

PUNCH ta ruwaito cewa Rundunar NDLEA ta Jihar Edo ta lalata gonakin tabar wiwi guda biyu, waɗanda aka kiyasta za su samar da kilogiram 4,628.9 na tabar wiwi, tare da kama wasu mutane 10 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a wasu ayyuka daban-daban a faɗin jihar.

Kwamandan NDLEA na Jihar Edo, Mitchell Ofoyeju, ya bayyana hakan ranar Litinin, inda ya ce an gudanar da ayyukan ne bisa sahihan bayanan sirri.


A cewarsa, gonar farko da ke Ugboku, dajin Igbanke, a Ƙaramar Hukumar Orhionmwon, tana da girman hekta 0.699792, kuma an kiyasta cewa za ta samar da kilogiram 1,749.26 na tabar wiwi. Ya ce an kama wani mutum mai shekaru 40, Agholor Elebojie, bisa alaƙa da gonar.

Ofoyeju ya ƙara da cewa gonar ta biyu tana da girman hekta 1.151889, inda aka kiyasta za a samu kilogiram 2,879.7225 na tabar wiwi, kuma an lalata gonar. Ya ce jami’an sun kuma kwato buhuna biyu na tabar wiwi da aka sarrafa, masu nauyin kilogiram 12.4, daga gonar ta biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM