NE

News Elementor

Ƙasar Birtaniya Ta Jagoranci Tattaunawa Da Ƙasashe 40 Domin Neman Mafita Kan Buɗe Mashigar Hormuz

Birtaniya ta jagoranci tattaunawa da ƙasashe 40 kan matakin bai ɗaya da ya kamata su ɗauka don buɗe mashigin Hormuz da Iran ta rufe, tare da dakatar da garkuwar da Tehran ta yiwa tattalin arziƙin duniya.

Ministar harkokin wajen Birtaniya Yvette Cooper da ta jagoranci ganawar da aka yi ta bidiyo, wadda ta ƙunshi wakilan ƙasashen Faransa, Jamus, Canada, Daular Larabawa da kuma Indiya, ta ce Iran ta nuna halin ko in kula da rufe mashigin Hormuz wanda ya yi matuƙar tasiri ga rayuwar miliyoyin iyalai da kasuwanci a dukkan sassan duniya.

A zantawarta da manema labarai gabanin su fara tattaunawar cikin sirri, Cooper ta ce sun shaida yadda Iran ta rufe Hormuz da gangan, don yin garkuwa da tattalin arziƙin duniya,.

Tattaunawar ta zo ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya ce batun buɗe mashigin Hormuz haƙƙi ne da ya rataya a wuyan ƙasashen da suka dogara dashi.

Duk da cewa sun ƙare taron ba tare da cimma wata taƙamaiman matsaya ba, amma sun amince cewa bazamu lamunci Iran ta ƙaƙabawa jiragen ruwan da ke shige da fice a mashigin Hormuz haraji ba.

Tun da fari dai shugabannin na Turai sun ƙi amincewa da buƙatar Trump na aike wa da dakarunsu yankin Gabas ta Tsakiya, saboda fargabar jansu cikin yaƙin da ba su suka faro shi ba, to sai dai tasirin rikicin wanda ya haifar da tashin farashin makamashi ya tilasta musu haɗa kai don ganin yadda za su kare manufofinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM