Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama Gambo Hassan mai shekara 53 bisa zargin satar mutane, fyade, fashi da makami da mallakar makami ba bisa ka’ida ba.
Acikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, Nafiu Habib, ya fitar a ranar Lahadi, 13 ga Satumba, 2026.
Rundunar ta ce jami’anta sun kama Gambo Hassan, wanda ake kira Anahaka, a kan titin Adamu Jumba da misalin ƙarfe 8:45 na daren 11 ga Satumba, inda ake zarginsa da ɓadda kama a matsayin ɗan acaba da yamma domin ɗaukar fasinjoji, musamman mata, tare da yi musu fashi.
Sanarwar ta ce, binciken farko ya kai ga gano mata 15 da ake zargin ayyukansa suka shafa, kafin adadin ya ƙaru zuwa 35, sannan binciken gidansa ya kai ga ƙwato wayoyi, ƙuɗi ₦425,435, da wasu kuɗaɗen Kenya da Turkiyya da sauran kayayyaki.
Rundunar ta ce an miƙa wanda ake zargin da kayayyakin da aka ƙwato zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar Bauchi domin ci gaba da bincike, tare da neman waɗanda lamarin ya shafa su fito domin bayar da bayanan da za su taimaka wa binciken.