NE

News Elementor

An ceto ɗaliban kwalejin fasaha ta Kaura Namoda guda 4 da aka sace a Zamfara

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ceto sauran dalibai huɗu na Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Kaura Namoda a Jihar Zamfara, waɗanda aka sace daga gidansu a ranar 2 ga Yuni.

Daliban, waɗanda suka ƙunshi maza uku da mace ɗaya, an sako su ne a daren Laraba yayin wani samame da aka gudanar bisa ga bayanan sirri, ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

Rahotanni sun ce an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da satar daliban yayin aikin, yayin da aka kashe wasu daga cikin masu garkuwar da mutanen.

Daliban na cikin ɗalibai bakwai da aka sace bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari gidan da suke zaune a yankin Low-Cost da ke garin Kaura Namoda.

Da yake magana da jaridar TheCable bayan harin, kakakin rundunar ’yan sandan Zamfara, Yazid Abubakar, ya ce ɗaya daga cikin daliban ya tsere a lokacin harin, wanda ya bar wasu shida a hannun masu garkuwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM