NE

News Elementor

Dan takarar gwamnan na jam’iyyar ADC a jihar Sokoto Manir Dan’iya ya yi Alla- wadai da sace Mutane sama da 50 a Mahaifar Mataimakin gwamnan jihar Sokoto

Ɗan takarar gwamnan jihar Sakkwato na jam’iyyar ADC, Hon. Manir Muhammad Dan’iya, ya yi Alla-wadai da rahotannin sace mutane sama da 50 a Garin Idi, mahaifar mataimakin gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Idris Muhammad Gobir, yana mai cewa lamarin ya nuna yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara a jihar.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Aminu Abdullahi, ya fitar, Dan’iya ya ce hare-haren ‘yan bindiga sun kai matsayin da har al’ummomin da ke da alaƙa da manyan jami’an gwamnati ba su tsira daga hare-haren masu aikata laifuka ba.

Ya bayyana cewa yawaitar hare-haren ‘yan bindiga, sace-sacen mutane, kashe-kashe da raba jama’a da muhallansu na nuna cewa gwamnatin tarayya da ta jihar Sakkwato ba su cika nauyin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya ɗora musu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba.

Dan’iya ya ce abin takaici ne rahotannin da ke cewa mazauna Garin Idi sun shiga tattaunawa kai tsaye da ‘yan bindiga tare da tara kuɗi domin kuɓutar da mata, tsofaffi da almajirai da aka sace. Ya ce idan hakan gaskiya ne, to yana nuna irin halin ƙunci da al’ummomin da abin ya shafa ke ciki, tare da nuna buƙatar ƙara jami’an tsaro, inganta tattara bayanan sirri da saurin kai ɗauki a yankunan da ke fama da hare-hare.

Ya kuma nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnatin jihar ke mayar da martani kan matsalar tsaron da ke addabar ƙananan hukumomi da dama, yana mai cewa hare-haren sun jawo asarar rayuka, durƙusar da harkokin noma, raba iyalai da muhallansu da kuma ƙara tsoro a tsakanin jama’a.

Ɗan takarar gwamnan ya buƙaci gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar Sakkwato da hukumomin tsaro su ƙara zage damtse wajen murƙushe masu aikata laifuka, ƙarfafa tsaro a yankunan da ke cikin haɗari tare da tabbatar da kamo waɗanda ke da hannu a hare-haren domin su fuskanci hukunci.

Haka kuma, ya yi kira da a ƙara tallafa wa al’ummomin da abin ya shafa ta fuskar agajin jin ƙai da matakan tsaro domin su samu damar komawa gidajensu cikin kwanciyar hankali.

Dan’iya ya jajanta wa al’ummar Garin Idi da sauran yankunan da matsalar tsaro ta shafa, tare da addu’ar Allah Ya kare Jihar Sakkwato, Ya ba jami’an tsaro nasara a aikinsu, sannan Ya dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM