NE

News Elementor

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta gargadi masu neman shiga auren gata su yi hattara da ƴan damfara

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta gargadi al’umma da kada su biya kuɗi ga duk wanda ya yi iƙirarin zai taimaka musu wajen yin rajista a shirin auren gata na jihar, tana mai bayyana irin wannan buƙata a matsayin damfara.

Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar, Dakta Mujahideen Aminuddeen, ne ya bayar da wannan gargaɗi a Kano.

Ya ce hukumar ta samu rahotannin cewa wasu mutane na karɓar kuɗi daga masu son cin gajiyar shirin, duk da cewa Gwamnatin Jihar Kano ta yanke shawarar ɗaukar nauyin shirin gaba ɗaya.

Dakta Aminuddeen ya jaddada cewa babu wanda Hukumar Hisbah ko Gwamnatin Jihar Kano ta ba izinin karɓar kuɗin rajista ko wani nau’in kuɗi daga masu son shiga shirin.

Ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ɗaukar nauyin shirin auren gatw, wanda ya haɗa da kayan aure, kayan ɗaki, jigilar kayan ɗakin da kuma jarin fara sana’a ga waɗanda za su amfana.

A cewarsa, shirin kyauta ne, don haka ya kamata masu neman shiga su yi watsi da duk wanda ke neman a biya shi kuɗi ko kuma ya yi alƙawarin samar musu da gurbi a madadin kuɗi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM