Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutane uku da ake alaƙantawa da sace ɗalibai da malamai a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo hukuncin daurin rai da rai.
Mai shari’a Salim Ibrahim ya umarci cewa hukuncin ya fara aiki tun daga ranar da aka kama waɗanda aka yanke wa hukuncin.
Lauyan masu kare waɗanda ake tuhuma ya roƙi kotun da ta yi sassauci, yana mai cewa wannan ne karo na farko da suka aikata laifi kuma sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da su.
Sai dai lauyan gwamnati ya yi watsi da wannan roƙo, yana mai cewa waɗanda aka yanke wa hukuncin sun san mutanen da suka aikata laifin satar mutane, amma maimakon su kai rahoto ga hukumomin tsaro, sai suka ɓoye bayanan.
Bayan sauraron ɓangarorin biyu, kotun ta yanke wa mutum ukun hukuncin daurin rai da rai.