INECShugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa hukumar za ta kasance mai tsaka-tsaki wajen gudanar da babban zaɓen shekarar 2027.
Amupitan ya ce INEC ba ta da wani ɗan takara ko jam’iyyar siyasa da take fifitawa, yana mai jaddada cewa alhakin hukumar shi ne tabbatar da an mutunta ra’ayin masu zaɓe na Najeriya.
Ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai wajen Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, a Zariya, Jihar Kaduna, a matsayin wani ɓangare na ci gaba da ganawa da masu ruwa da tsaki da kuma shirye-shiryen hukumar na zaɓen shekarar 2027.
Ziyarar ta kuma kasance wani ɓangare na tantance matakin shirye-shiryen hukumar a shiyya tare da shirin gudanar da tattaunawa da ma’aikatanta, yayin da INEC ke ƙara ƙaimi wajen shirye-shiryen gudanar da zaɓen a faɗin ƙasar.
Ya bayyana sarakunan gargajiya a matsayin muhimman masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe, yana mai nuni da irin tasirinsu da kuma yadda suke da kusanci da al’ummomi a sassa daban-daban.
Ya ce zaɓe a asali ya shafi alaƙar da ke tsakanin ’yan ƙasa da mutanen da aka damƙa wa alhakin riƙe muƙaman gwamnati, yana mai cewa amincewar jama’a na da matuƙar muhimmanci wajen samun nasarar dimokuraɗiyya.
A cewar shugaban INEC, hukumar ta fara shirye-shiryen zaɓen tun da wuri saboda girma da kuma sarkakkiyar aikin gudanar da zaɓe a faɗin Najeriya.