NE

News Elementor

Bala Wunti ya musanta zargin ɓatan Naira Biliyan 210 a kamfanin mai na NNPC

Tsohon shugaban hukumar kula da zuba jari ta man fetur a Nigeria, Bala Wunti, ya musanta ikirarin cewa Naira tiriliyan 210 sun ɓace daga asusun Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPC.

Ya ce cikakken nazarin bayanan kuɗin kamfanin na shekarar 2023 da aka tantance bai gano irin wannan gibin ba.

Da yake bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa da ke nazarin asusun NNP na shekarar 2023, Wunti ya ce zargin bacewar kuɗin ya samo asali ne daga rashin fahimtar ƙa’idojin lissafin kuɗi, ba daga wata shaidar almundahana ba.

A cewarsa, adadin da ya jawo ce-ce-ku-ce ya samo asali ne bayan an haɗa bayanai biyu daban-daban na ma’aunin kuɗi da bai kamata a haɗa ba.

Ya bayyana cewa kusan Naira tiriliyan 107 kuɗaɗe ne da ake bin NNPC., yayin da Naira tiriliyan 103 kuwa kuɗaɗen bashin da kamfanin ke bin wasu ne.

Bisa binciken da ya gudanar da kansa, Wunti ya bayyana ƙarƙashin rantsuwa cewa babu wata hujja ta gaskiya da ke nuna cewa Naira tiriliyan 210 sun ɓace daga littattafan kuɗin kamfanin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM