Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta soke hukuncin wata babbar kotun tarayya da ta ce hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC, ba ta da ikon tsara jadawalin gudanar da zaɓen fidda gwani da kuma tsayar da ƴan takara gabanin babban zaɓen 2027.
A hukuncin da alkalan kotun suka yanke baki a ranar Alhamis, kotun ta tabbatar da cewa jadawalin da INEC ta fitar na shirye-shiryen zaɓen 2027 yana nan daram.
Yayin karanto hukuncin, Mai Shari’a Okon Abang, ya ce jam’iyyar Youth Party (YP), wadda ta shigar da ƙarar, ba ta da hurumin kalubalantar jadawalin INEC.
Kotun ta ce jam’iyyar ta kasa bayyana yadda jadawalin da INEC ta fitar ya tauye mata haƙƙinta ko ya hana ta gudanar da zaɓen fidda gwani domin shiga zaɓen 2027.
Saboda haka, kotun ta yanke hukuncin cewa INEC tana da iko a doka ta fitar da jadawalin zaɓen, tare da cewa babbar kotun tarayya ta yi kuskure lokacin da ta amince da buƙatun da jam’iyyar ta gabatar.
Kotun ta kuma ce jam’iyyar siyasa za ta iya zuwa kotu ne kawai idan an take haƙƙinta na shiga zaɓen 2027.
A watan Mayu ne, Babbar Kotun Tarayyar da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa INEC ba ta da ikon sanya wa jam’iyyun siyasa lokacin da za su gudanar da zaɓen fidda gwani ko tsayar da ƴan takara.