NE

News Elementor

Gwamnatin tarayya ta karyata rahotannin da ke cewa ministan tsaro General Christopher Musa na shirin yin murabus

A wani bayani da ofishin ministan ya fitar, ya bayyana rahotannin a matsayin karya, inda ya bukaci alumma su yi fatali da su.

Bayanin dai na dauke da sa-hannun hadimin ministan kan sha’anin yada labarai, Leah Katung-Babatunde.

A cewar bayanin, an ja hankalin ofishin kan wasu rahotanni da ake yadawa a shafukan sadarwa na zamani da ke ikirarin cewa, General Musa zai ajiye mukaminsa.

Ya jaddada cewa, General Christopher Musa ya mayar da hankalinsa wajan sauke nauyin da ke kansa, da kuma aiwatar da manufofin gwamnati a bangaren tsaro.

Gwamnatin ta kuma bukaci alumma su tantance gaskiyar zance kafin su yada shi ga duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM