Wani limamin cocin Katolika ɗan Najeriya, Benjamin Madu mai shekaru 54, ya rasu a jihar Massachusetts da ke Amurka, bayan rahotanni sun ce ya kashe kansa yayin da yake fuskantar matsalar ƙarewar takardar izininsa ta zama a ƙasar.
Rahotanni sun ce an same shi a gidansa ranar 2 ga Yulin 2026, makonni kaɗan kafin wa’adin takardar izinin aikinsa ta addini (R-1 visa) ya ƙare a ranar 29 ga Yuli.
An ce ƙoƙarin sabunta takardar izinin ya ci tura sakamakon sabbin matakan takaita shige da fice da gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ta ɗauka, lamarin da ya tilasta masa komawa Najeriya domin neman sabuntawa.
Kafin rasuwarsa, Madu ya bayyana wa mabiyansa cewa yana cikin damuwa kuma baya son komawa Najeriya saboda fargabar abin da zai iya fuskanta.
Bayan rasuwarsa, ƙungiyar US-Nigeria Civil Society Coalition ta buƙaci Shugaba Donald Trump da ya dakatar da korar ‘yan Najeriya daga Amurka, tare da bai wa waɗanda ke cikin haɗari kariyar zama ta wucin gadi (TPS).