NE

News Elementor

Kakakin majalisar wakillai, Abbas Tajudden, ya bukaci a fara kafa ‘yan sandan jihohi daya-bayan-daya a faɗin Nigeria

Kakakin majalisar wakillai, Abbas Tajudden, ya bukaci a fara kafa yansandan jihohi daya-bayan-daya a fadin Nigeria, inda ya ce bai kamata kowace jiha ta mallaki yansanda ba ba tare da ta cika sharudan da aka ayyana ba.

Abbas ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da jawabi a babban taro kan sha’anin tsaron kasa da aka shirya a wani bangare na makon majalisar tarayya a birnin Abuja.

Ya ce duk da cewa kwaskwarimar da ake yiwa kundin tsarin mulkin kasa zai sauya fasalin tsaro a Nigeria, amma kuma nasarar hakan ta ta’allaka ne kan samar da tsare-tsare na musamman, da bangaren kudi, da kuma yin hadaka mai ma’ana a tsakanin hukumomin tsaro na tarayya da na jihohi.

Kakakin majalisar ya bayyana matakin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka na mikawa majalisar kudurin zartaswa kan kafa rundunar yansandan jihohi a matsayin babban yunkuri wanda zai magance kalubalen tsaro a Nigeria.

Ya ce yanayin yadda ake samun karuwar jama’a a Nigeria da kuma fadadar matsalolin tsaro ya nuna cewa ba za a iya ci-gaba da tafiyar da tsarin yansandan tarayya ba kadai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM