NE

News Elementor

Kotu ta kwace kadarori 48 da ke da alaƙa da tsohon ministan shari’a Abubakar Malami

Kotu ta kwace kadarori 48 da ke da alaƙa da tsohon ministan shari’a Abubakar Malami

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin kwace kadarori 48, ciki har da wata jami’a, da ake alaƙanta wa ga tsohon antoni janar kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, tare da mayar da su hannun gwamnatin tarayya.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta ce hukumar EFCC ta tabbatar wa kotu cewa ana zargin kadarorin sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka, yayin da Malami ya kasa nuna hujjojin da ke tabbatar da cewa ya mallake su ta hanyar da ta dace.

Kotun ta kuma yi watsi da ƙorafe-ƙorafen Malami, iyalansa da wasu kamfanoni da ke da alaƙa da kadarorin, tana mai cewa ba su da tushe.

Sai dai kotun ta soke umarnin kwace wasu kadarori tara da ke jihohin Kebbi da Kaduna, bayan ta ce EFCC ta kasa tabbatar da cewa an mallake su ne ta hanyar haramtacciyar hanya.

Tun da farko EFCC ta nemi a kwace kadarori 57 da ta kiyasta darajarsu ta kai Naira biliyan 212.8, tana zargin an samo su ne daga haramtattun ayyuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM