Mai bai wa gwamnan jihar Kano shawara na Musamman kan harkokin matasa da wasanni, Hon. Sani Musa Danja, ya ce jihar ta samu amincewar Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya (IGP) domin haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin jihar Kano da shirin Police Campaign Against Cultism and Other Vices, wajen gudanar da babban shirin wayar da kan matasa a faɗin jihar.
A wata sanarwa da Hon. Sani Musa Danja ya fitar ranar 25 ga Yulin 2026, ya ce shirin zai mayar da hankali kan yaƙi da daba, shan miyagun ƙwayoyi, tashe-tashen hankula tsakanin matasa da sauran munanan ɗabi’u, tare da ƙarfafa kyawawan halaye da bin doka.
Sanarwar ta bayyana cewa amincewar, wadda aka isar da ita a hukumance mai ɗauke da kwanan wata 21 ga Yulin 2026, ta nuna amincewar Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya da ƙoƙarin Gwamnatin Kano wajen bunƙasa matasa, hana aikata laifuka da kuma inganta tsaron al’umma.
Ta ce shirin ya yi daidai da matakan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka domin ƙarfafa tsaro a jihar, ciki har da ƙaddamar da jwamitin haɗin gwiwa kan yaƙi da shan miyagun Ƙwayoyi, sanya hannu kan dokar zartarwa da ta haramta daba da sauran ayyukan ta’addanci, ƙarfafa aikin Neighbourhood Watch, da kuma ci gaba da shirye-shiryen ƙarfafa matasa ta fuskar ilimi, wasanni, koyon sana’o’i da samar da ayyukan yi.
Hon. Sani Musa Danja ya yabawa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda bisa amincewa da wannan haɗin gwiwa, yana mai jaddada aniyar gwamnatin jihar ta ci gaba da aiki tare da Rundunar ‘Yan Sanda, POCACOV da sauran masu ruwa da tsaki domin gina Kano mai zaman lafiya da tsaro.
A cewar sanarwar, shirin wayar da kan matasan zai shafi makarantu, manyan makarantun gaba da sakandare, al’ummomi, ƙungiyoyin matasa, sarakuna, malamai da ƙungiyoyin farar hula, domin inganta zaman lafiya, kishin ƙasa da mutunta doka.
Gwamnatin Kano ta kuma sake jaddada aniyarta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da ba matasa damar zama nagartattun ‘yan ƙasa masu bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.