NE

News Elementor

Sojoji sun ceto mutum 5 daga cikin iyalan shugaban karamar hukumar Bungudu yayin da ake ci gaba da kokarin kubutar da shi

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutum biyar daga cikin iyalan shugaban karamar hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, Alhaji Nura Umar Abdullahi, bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai gidansa tare da yin garkuwa da shi.

A cewar rundunar, sojoji sun isa wurin da gaggawa bayan jin karar harbe-harbe, inda suka fafata da maharan. Hakan ya tilasta wa ‘yan ta’addan barin matar shugaban ƙaramar hukumar, mahaifiyarsa, ‘ya’yansa biyu da wani ɗan uwansu, waɗanda aka ceto ba tare da sun ji rauni ba.

Sai dai maharan sun tsere da shugaban ƙaramar hukumar zuwa cikin daji. Harin ya yi sanadin mutuwar ‘yan sanda biyu, ɗan kungiyar sa-kai guda da wani farar hula, yayin da ɗan uwan shugaban ƙaramar hukumar ya samu raunuka.

Rundunar ta ce ta ƙaddamar da haɗaɗɗen samame tare da haɗin gwiwar ‘yan sanda, jami’an DSS da masu sa-kai domin ceto shugaban ƙaramar hukumar, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da farautar maharan har sai an kuɓutar da shi tare da gurfanar da masu hannu a harin a gaban doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM