NE

News Elementor

Gwamnatin Sokoto ta wanke kanta daga zargin alaƙa da boka mai Shaho

Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayyana cewa ba ta da wata alaƙa da wani mutum da ake kira Mai Shaho, bayan wani bidiyo da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta ya jawo ce-ce-ku-ce.

Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Sokoto, Abubakar Bawa, ya ce gwamnatin ta nisanta kanta gaba ɗaya daga mutumin da duk wasu ayyukansa.

A cewarsa, matakin ya biyo bayan wani faifan bidiyo da ake zargin Mai Shaho ya fitar, inda aka nuna shi yana binne bunsuru da ransa tare da yin wasu kalamai da suka shafi ɗan takarar gwamna na wata jam’iyyar siyasa a jihar.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin ba ta goyon bayan bokanci ko duk wani aiki da ya saɓa wa doka, kyawawan ɗabi’u da koyarwar addinin Musulunci.

Haka kuma, gwamnatin ta umarci Hukumar Hisbah ta Jihar Sokoto da ta ɗauki matakin da ya dace bisa tanadin doka kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM