Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin mutum 26 a manyan hukumomin 10 na gwamnatin tarayya, ciki har da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, wanda aka nada a matsayin shugaban hukumar samar da lantarki a yankunan karkara.
Mai Magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya sanar da nade-naden wadanda za su fara aiki nan take.
Fadar shugaban kasa ta ce Fayose zai jagoranci hukumar ta REA tare da Alhaji Ahmadu Abubakar da Engineer Ilyasu Ibrahim Makinta a matsayin wakillai, yayin da babban directan hukumar mai ci yanzu, Abba Aliyu Abubakar da directocinsa guda uku za su ci-gaba da rike mukamansu.
Tinubu ya kuma nada Major General Junaid Bindawa a matsayin shugaban hukumar biyan albashin manyan jami’an gwmanati tare da wasu mutum 8 a hukumar.
Bayanin ya kara da cewa, an nada wani tsohon dan majalisar wakillai daga jihar Legas, Olajumoke Okoya-Thomas a matsayin sakataren hukumar, yayin da aka nada Dr Ogbole Ene Lilian, Oladele Olatubosun da Yakubu Umar Barde a matsayin kwamishinonin hukumar daga jihohin Benue, Oyo da kuma Kaduna.