Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta hana sana’ar tura fina finai da ake kira “Downloading” a faɗin jihar.
Mataimakin babban Kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano, Dakta Mujahideen Aminudeen ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikowa Daily Nigerian Hausa a ranar Alhamis.
Acewarsa, hukumar ta hana tura fina finan ne bayan ta gano cewa, wasu na amfani da hakan wajen tura bidiyoyin batsa.
“Duba da korafe-korafen da aka samu daga wajen al’umma inda ake samun bata gari wajen cajin waya su ke yin downloading wasu fina finai, ko wasu bidiyoyi na batsa, suna basaja da tura wa’azin Malamai, amma idan ka buɗe sai ka ga fim din batsa ne”.
Dakta Mujahideen Aminudeen ya ƙara da cewa, wasu fina finan ma da ake turawa basu cancanci yara kanana su kalla ba, kuma kallon su na bata musu tarbiya.
“Yara waɗanda shekarun su ba su kai sun kawo ba, ana tura musu wadannan fina finai da za su bata tarbiyar su”.
Duba da hakan, hukumar ta Hisbah ta ce ta haramta tura fina finai a faɗin kananan hukumomi 44 na jihar kuma za ta fara kama duk waɗanda su ka bijerewa dokar.