NE

News Elementor

kwastam ta tara Naira Biliyan 63.07 a Kano da Jigawa cikin watanni 6

Hukumar Kwastam ta shiyyar Kano da Jigawa ta sanar da cewa ta tara kudaden shiga na Naira biliyan 63.07 tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2026.

Mukaddashin Kwanturolan shiyyar, Usman Umar Adamu, ya bayyana cewa adadin ya fi na makamancin lokacin shekarar 2025 da Naira biliyan 4.6, wanda ke nuna karin kashi 7.4 cikin 100.

Ya kuma ce yankin kasuwanci na musamman na Kano (Free Trade Zone) ya samar da sama da Naira biliyan 26 a watanni shida na farko na shekarar, yayin da aka kuma kwato kusan Naira biliyan 3 sakamakon take dokokin jigilar kaya.

Adamu ya ce rundunar ta kama kwantena 14 da aka karkatar da su ba bisa ka’ida ba, tare da kwace motoci, shinkafa, taliya, man girki da sauran haramtattun kayayyaki da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.7.

A cewarsa, an kama mutane 22 da ake zargi da hannu a laifukan, inda aka mika wasu ga hukumomin tsaro domin ci gaba da bincike, yayin da aka bayar da belin wasu. Ya tabbatar da cewa Kwastam za ta ci gaba da ƙarfafa yaki da fasa kwauri tare da inganta kasuwanci na halal da tara kudaden shiga ga gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM