Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa aikin noman ciyawar alfafa (Premium Alfalfa) da kamfanin Jigawa El-Meena Farms (JEFs) ke gudanarwa a Jihar na iya zama mafita mai ɗorewa ga rikicin manoma da makiyaya a Najeriya.
Shettima ya bayyana hakan ne a yayin da ya ziyarci rumfar baje kolin kamfanin a babban taron Tattalin Arziki da Zuba Jari na Jihar Jigawa, (J-Invest 2026) da aka gudanar a Dutse.
A cewarsa samar da ciyawar alfafa a babban sikeli zai tabbatar da wadataccen abincin dabbobi, rage dogaro da kiwo a fili, tare da inganta tsarin kiwon dabbobi na zamani.
“Tare da wannan gagarumin aikin noman ciyawar alfafa mai inganci da kamfanin Jigawa El-Meena Farms ke gudanarwa, rikicin manoma da makiyaya zai iya zama tarihi,” in ji Mataimakin Shugaban Ƙasar.
Ya ƙara da cewa, irin wannan zuba jari zai taimaka wajen bunƙasa samar da abinci, ƙarfafa zaman lafiya da kuma haɓaka tattalin arzikin ƙasa.
Masana sun ce wadataccen abincin dabbobi mai inganci zai ƙarfafa tsarin kiwon dabbobi na zamani, tare da rage matsin lamba kan filayen noma da albarkatun ruwa, waɗanda ke haddasa rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya.
Kamfanin Jigawa El-Meena Farms na da burin samar da ciyawar alfafa domin biyan buƙatun masana’antun madara da kiwon dabbobi, tare da mayar da Jigawa cibiyar samar da abincin dabbobi da fitar da shi zuwa ƙasashen Yammacin Afirka.
Taron J-Invest 2026 ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, masu zuba jari, abokan hulɗar ci gaba da shugabannin kasuwanci, inda aka baje kolin damammakin zuba jari a fannoni daban-daban na tattalin arziƙi.
Shettima ya kuma jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na samar da kyakkyawan yanayi ga masu zuba jari da tallafa wa ayyukan da za su bunƙasa samar da abinci da ayyukan yi ga al’umma.