NE

News Elementor

Yan bindiga sun kai hari da rana tsaka, inda suka kashe sama da mutum 22 tare sace dabbobi a ƙauyen Sauna da ke karamar hukumar Talata Mafara.

Wani mazauni garin Sauna da ya zanta da lconic FM Nigeria wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yan bindigar sun kai harin ne da rana tsaka inda suka mamaye ƙauyuka da dama dake karkashin mazaɓar Sauna.

Ya ce da farko sun yi kokarin shiga garin Sauna amma bayan musayar wuta da ƴan banga sai suka ja baya.

A cewarsa, yan bindigar sun sace dabbobi masu tarin yawa bayan da suka mamaye garuruwa irinsu Zauren Goro, Tulluwa, Unguwar Shanu, Tsangaya, Tudun Namali da kuma Tungar Dahiru.

Haka kuma, ya ce sun kashe mutane da ba a san adadinsu ba a lokacin harin, inda ya ce a gabansa an ɗauko gawar sama da mutum 22 kuma yanzu haka ana ci gaba da neman sauran mutane saboda yan bindigar sun rutsa da manoma ne a lokacin da suke aiki a gonakinsu.

Ya ce lamarin ya fara tun karfe 2:20pm na rana amma jami’an tsaro ba su kai masu ɗauki ba sai da karfe 4:40pm bayan ƴan bindigar sun wuce

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM