NE

News Elementor

Majalisar Dattawa Za Ta Tattauna Batun Ware wa Hukumar Bogi Naira Biliyan 1.3 A Kasafin Ƙudin 2026

Ana sa ran Majalisar Dattawan Najeriya za ta tattauna cece-kucen da suka biyo bayan ware wa wata hukuma da ake zargi da kasancewa bogi mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council kuɗi har Naira biliyan 1.3 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, a zamanta na ranar Talata.

Jaridar The PUNCH ta ruwaito cewa batun ya janyo cece-kuce bayan bayanai sun nuna cewa an saka wa hukumar kuɗaɗen kasafi duk da zargin cewa ba halastacciyar hukuma ba ce.

Rahotanni sun kuma nuna cewa an karɓi wata wasiƙar naɗi ta bogi mai ɗauke da sa hannun jabu na Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, a Hedikwatar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ba tare da cikakken tantancewa ba.

Lamarin ya bai wa wani mutum mai suna Prince Adeniyi Adeyemi Mathew damar samun ofishi a rukunin Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja, inda hukumar ta ci gaba da aiki kamar halastacciyar hukuma ta gwamnati na fiye da shekara guda.

Ana sa ran tattaunawar Majalisar Dattawa za ta mayar da hankali kan yadda aka samu wannan tangarɗa da matakan da za a ɗauka kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM