Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan abin da ya kira jagoranci mai ƙarfi wajen yaƙi da ta’addanci da matsalolin tsaro a Najeriya.
A wata wasiƙa da ya aike wa Tinubu mai kwanan wata 6 ga Yuli, 2026, Trump ya ce yana goyon bayan ƙudirin gwamnatin Najeriya na magance hare-haren ‘yan ta’adda, musamman waɗanda ke shafar al’ummomin Kiristoci.
Ya kuma ce haɗin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya na ci gaba da ƙarfafa, inda ƙasashen biyu suka kafa Kwamitin Haɗin Gwiwa kan Tsaro domin musayar bayanan sirri, horas da jami’an tsaro da gudanar da ayyukan haɗin gwiwa.
A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, haɗin gwiwar ya taimaka wajen kai farmaki kan maɓoyar ISIS a yankin Tafkin Chadi a watan Mayu, inda aka kashe babban jagoran ƙungiyar, Abubakar Al-Minoki, da wasu manyan kwamandojinta.
Trump ya kuma tabbatar da aniyar Amurka na ci gaba da haɗa kai da Najeriya wajen yaƙi da ta’addanci da inganta tsaron ƙasar.