NE

News Elementor

Shugaban ƙasa Bola Tinubu zai jagoranci taron ma’adinai na Afirka a ƙasar Amurka

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai jagoranci wani babban taron ƙasashen Afirka kan bunƙasa ma’adinai masu muhimmanci a birnin New York na Amurka a watan Satumba.

Taron, wanda za a gudanar a ranar 21 ga Satumba, zai gudana ne a gefen taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.

Tinubu, wanda shi ne shugaban babban taron ƙungiyar Africa Minerals Strategy Group, zai jagoranci taron da zai haɗa shugabannin Afirka, ministoci, masu zuba jari da hukumomin samar da kuɗaɗen raya ƙasa, da kuma shugabannin kamfanonin ma’adinai, fasaha da sufuri.

Taken taron shi ne “Daga Albarkatun Ƙasa zuwa Arziki: Haɗin Kan Afirka wajen Ƙara Darajar Ma’adinai.”

Ƙungiyar ta ce taron zai mayar da hankali ne kan yadda ƙasashen Afirka za su daina fitar da ma’adinai a matsayin ɗanyen kaya kawai, su mayar da hankali wajen sarrafa su a cikin nahiyar domin ƙara samun kuɗaɗen shiga, ayyukan yi da bunƙasa masana’antu.

Afirka na da dimbin ma’adinai da suka haɗa da lithium, jan ƙarfe, cobalt, graphite, manganese da wasu ma’adinai na musamman da ake buƙata wajen kera motocin lantarki, makamashi mai sabuntawa, fasahar zamani da na’urorin tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM