Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto ta ce ta samu gagarumar nasara a ci gaba da yaƙi da ‘yan bindiga da masu aikata laifukan sata, inda ta dakile wani hari da ake zargin ‘yan Lakurawa ne suka kai, ta kuma kwato shanu 11 da aka sace tare da cafke wasu da ake zargi da hannu a satar kayayyaki da babura.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, ya fitar, ya ce jami’an rundunar na yankin Tangaza, tare da jami’an Yaƙi da Garkuwa da Mutane sun yi gaggawar kai dauki bayan samun kiran gaggawa cewa wasu da ake zargin Lakurawa ne sun kai hari kauyen Ayawa da ke Karamar Hukumar Tangaza tare da sace shanu 11.
Sanarwar ta ce jami’an tsaron sun tare hanyoyin da maharan za su iya bi wajen tserewa, sannan suka fafata da su.
Daga bisani maharan sun tsere zuwa cikin daji bayan sun bar shanun da suka sace, inda aka kwato dukkansu tare da mayar da su ga masu su.
A wani samame na daban, rundunar ta ce jami’anta na Strike Force sun cafke mutane hudu da ake zargi da hannu wajen satar atamfofin mata guda 53 daga wani shago da ke unguwar Guiwa Low Cost a cikin birnin Sokoto.
‘Yan sanda sun ce daya daga cikin wadanda aka kama, Mustapha Danbaba, ya amsa laifin fasa shagon da satar atamfofin, sannan bincike ya nuna cewa an sayar da kayayyakin da taimakon wasu da ake zargi.
Haka kuma, rundunar ta sanar da kama wani da ake zargi memba ne na kungiyar masu satar babura, bayan korafe-korafen da mazauna yankin Gidan Masau da wasu unguwanni suka shigar kan sace musu babura.
A cewar rundunar, wanda ake zargin mai suna Kabiru Abubakar ya amsa cewa shi da wani da har yanzu ake nema sun haɗa baki wajen satar babura daga yankunan Mana Babba, Nakasari, Bado Quarters, Gidan Kanawa da Tamaje.
Rundunar ta ce an samu nasarar kwato babur guda daya, yayin da ake ci gaba da bincike.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Sokoto, CP Hassan Hayatu Shaffa, ya yabawa jami’an da suka gudanar da wadannan ayyuka bisa jajircewarsu, tare da jaddada kudirin rundunar na ci gaba da yaƙi da miyagun laifuka da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.