NE

News Elementor

Latest Posts

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun daƙile wani yunƙuri da mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka yi na tatsar kuɗin haraji a jihar Yobe

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce bayanan sirri da dakarun suka samu sun nuna cewa ‘yan ta’addan na amfani da wasu motoci da babura wajen tattara kuɗaɗe daga fararen hula a yankin. Rundunar ta ce bayan samun bayanan sirrin, dakarunta suka gudanar da sintiri na musamman a yankin Paya Kafiya ranar...
Read more

Mun sanya hannu kan yarjejeniyar cewa Obi wa’adi daya kacal zai yi idan ya lashe zaɓe – Kwankwaso

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya tabbatar da cewa ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar, Peter Obi, ya sanya hannu kan yarjejeniyar yin wa’adi ɗaya na shekaru huɗu kacal idan ya lashe zaɓen 2027. Kwankwaso ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na...
Read more

Gwamnatin tarayya ta karyata rahotannin da ke cewa ministan tsaro General Christopher Musa na shirin yin murabus

A wani bayani da ofishin ministan ya fitar, ya bayyana rahotannin a matsayin karya, inda ya bukaci alumma su yi fatali da su. Bayanin dai na dauke da sa-hannun hadimin ministan kan sha’anin yada labarai, Leah Katung-Babatunde. A cewar bayanin, an ja hankalin ofishin kan wasu rahotanni da ake yadawa a shafukan sadarwa na zamani...
Read more

Yan sandan jihar Niger sun kama mutum biyu da ake zargi da safarar mutane

Rundunar yansandan jihar Niger ta kama mutum biyu da ake zargi da safarar mutane, inda ta ceto yan mata 9 da wani jinjiri dan wata 4 da aka kwace a hannun mahaifiyarsa a cikin garin Minna.  A wani bayani da kakakin rundunar, SP Abiodun Wasiu ya fitar, ya ce a ranar 9 ga watan Yuli, jami’an ofishin yansanda na Madalla dake aikin sintiri kan hanyar Madalla zuwa Suleja, sun kama wani mai suna Dauda Ayuba dake zaune a kauyen Kaffin-Koro a karamar hukumar Paikoro, inda ya ke kokarin safarar yan mata 6, yan tsakanin shekara 7 zuwa 13.  A lokacin bincike, Ayuba ya ce ya taso ne daga Benin na jihar Edo, bayan ya kulla harkalla da wata mata mai suna Iyee da wasu mutum 2 a kasuwar Ogbu, wadanda yanzu haka suka tsere, domin a kawo musu yaran.  A cewar Ayuba, ya karbi naira 194,000 a matsayin kudin sufuri domin kai yaran a Benin, inda za su yi aikatau da talla.  Ayuba ya ce ya yaudari iyayen yaran ne a kauyen Senchi, ta hanyar yi musu alkawarin saka yaran a makaranta, kazalika ya ce zai samu kamishon naira 10,000 ga kowace yarinya da za a biya albashin naira 20,000.  kg
Read more
1 … 27 28 29 30 31 … 56

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM